World News
Trending

Yadda Na Ke Kai Wa Yan Ta’adda Kayan Abinci Da Kudin Fansa A Zamfara – Wanda Ake Zargi yayi bayani.

Yadda Na Ke Kai Wa Yan Ta’adda Kayan Abinci Da Kudin Fansa A Zamfara – Wanda Ake Zargi yayi bayani.

Rundunar yan sanda a Jihar Zamfara sun yi nasarar kama wasu mutane da ake zargin suna kai wa yan bindiga makamai, kayan abinci da karbo kudin fansa Alhassan Lawali, wani wanda ake zargin da aka kama ya amsa cewa ya dade yana kai wa yan bindiga babura a daji suna biyan shi kasonsa Lawali ya ce yana sayarwa yan bindigan kowane babur kan N750,000 shi kuma suna bashi la’adar N15,000 sannan shine ke yi wa yan bindigan gyara idan babur dinsu ya lalace.

Alhassan Lawali, wani da ake zargi dan leken asirin yan bindigan Zamfara ne ya bayyana yadda ya rika kai wa yan bindiga kudin fansa da kayan abinci.

Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara, ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce:

“Yayin amsa tambayoyi, wanda ake zargin (Lawali) ya amsa cewa ya kai wa yan bindigan babura fiye da 14 a daji kan N750,000 kowannensu, inda ya ke samun N15,000 kan kowane babur. Wanda ake zargin ya kara da cewa tsawon shekaru, shi ke gyara wa yan bindigan baburan.

“Wanda ake zargin, cikin sanarwarsa, kuma ya ambaci wani Mansur Usman a matsayin abokin harkallarsa, wanda shima daga baya yan sanda sun kama shi.”

Da ake masa tambayoyi:

“Ya amsa cewa ya dade yana kai wa yan bindigan kayan abinci a daji. Ya kuma ce lokuta da dama, ya karbo wa yan bindigan kudin fansa. Kudin fansan na karshe da ya karbo shine N2.3m”.

Yan sandan sun kuma kama wani wanda ake zargin, wanda ya yi ikirarin shi soja ne dauke da bindigan, kayan sojoji, katin shaida na karya da wasu makamai masu hatsari a ranar Laraba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button