Naija-News
Trending

‘Matan da ƴan bindiga suka yi wa fyaɗe a Katsina sun haifi ƴaƴa fiye da 500,000’

Binciken wasu dattawan arewacin Najeriya na cewa ƴaƴan da aka haifa sakamakon fyaɗe da ‘yan fashin daji ke yi wa mata a yankunan Katsina zuwa Zamfara sun kai rabin miliyan.

Ɗaya daga cikin shugabannin dattawan na Katsina, Dr Bashir Kurfi ne ya shaida haka a wata hira da ya yi da BBC, kan matsalar tsaro a yankunan arewacin Najeriya, musamman katsina da Zamfara.

Dr Kurfi ya ce binciken da suka aiwatar cikin shekarun da aka kwashe ana yaƙi da ‘yan fashin daji, ya tabbatar musu da wadannan alkaluma sakamakon rahotanni da suka tattara daga kauyuka.

Ya ce mata da dama na kawo ƙorafinsu da kuma bayanai kan irin mutanen da suke yi musu fyade.

Yankunan Batsari da Dutsenma da Kankiya da Chiranci da su Funtua, Safana da dai sauransu duk ana samun irin wannan matsala a Katsina.

Ya ce a baya kafin matsalolin tsaro sai motoci 20 zuwa 50 su je Kano a rana ko daga Sokoto zuwa Kano ko ƙasashen makwabta, amma yanzu an daina, ‘yan kasuwa sun daina tafiya saboda haɗari da

To Allah de yakyauta yarufa mana asiri

Ameen summa ameen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button