World News

An kai hari kan mutumin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad a ƙasar Amurka.

An kai hari kan mutumin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad a ƙasar Amurka.

Marubuci dan kasar Birtaniya Salman Rushdie wanda Iran ta bukaci hallaka shi saboda rubutun batancin da ya yi wa Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam shekarun da suka gabata, ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin da aka kai masa a wannan Juma’ar a birnin New York na Amurka, inda aka daba masa wuka a wuyansa.

Faifan bidiyon da aka nuna a kafofin sada zumunta ya nuna yadda mutane suka ruga domin kai masa agaji bayan an kai masa harin a yankin Chautauqua, yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da cewar an daba masa wukar, ba tare da bayyana wanda ya kai harin ba.

Wani shaidar gani da ido ya wallafa cewar, wani mummunan abu ya faru a cibiyar Chautauqua – an kai wa Salman Rushdie hari akan dandali – yanzu haka an kwashe mutanen da ke dandalin.

Shugaban jami’an tsaron yankin ya tabbatar da cewar, an daba wuka lokacin harin, ba tare da karin haske akai ba.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan halin da Rushdie ke ciki.

Marubucin mai shekaru 75 ya yi suna lokacin da ya wallafa littafinsa mai suna ‘Midnight’s Children‘ a shekarar 1981, wanda daga bisani ya lashe kyautar duniya da ta Birtaniya saboda yadda ya labarta kasar India bayan samun yancin kanta.

Littafin da ya jefa Rushdie cikin fargaba

Amma kuma littafinsa da ya yi wa lakabi da ‘Satanic Verses‘ a shekarar 1988 ya haifar masa da matukar matsala, abin da ya kai ga shugaban addinin Iran Ayatullah Ruhollah Khomenei ya yanke masa hukuncin kisa saboda yadda littafin ya ci zarafin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Kada kumanta kuma tare da shafin APS News Hausa dake jihar jigawa,kucigaba da bibiyarmu domin samun sabbin rahotanninmu.

Kudanna mana alamar subscribe domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button