Political News
Trending

Yadda Aka Sace Miliyan 31 A Gidan Gwamnatin Katsina

Yadda Aka Sace Miliyan 31 A Gidan Gwamnatin Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa an sace miliyoyin kudi a gidan gwamnatin jihar.

Daya daga cikin hadiman gwamnan kan harkokin yada labarai, Al-Amin Isa ne, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.

Isah, wanda bai bayyana adadin kudaden da aka sace ba, ya ce tuni ‘yan sanda suka yi wa wasu daga cikin wadanda ake zargi tambayoyi.

Rahotanni sun bayyana cewar wadanda ake zargin sun yi awon gaba da Naira miliyan 31 daga ofishin mai kula da harkokin kudi na gidan gwamnatin jihar.

An kuma tattaro cewa wannan shi ne karo na biyu a wannan shekara da ake sace kudi a gidan gwamnatin jihar.

A watan Janairun 2020, an yi wa ofishin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa sata, inda aka sace Naira miliyan 16.

Kazalika, a watan Yulin 2022, wasu ‘yan bindiga sun harbe Aminu Darma, mai karbar kudi a ofishin sakataren fadar gwamnatin jihar tare da yin fashin Naira miliyan 61 a babban birnin jihar.

Related search

Mutane da dama sun mutu yayin wata zanga-zanga a ƙasar Saliyo.

 

Yadda Kwadayi Ya Kai ’Yan Najeriya Tashar Wulakanci A Aljeriya

Mutane da dama sun mutu yayin wata zanga-zanga a ƙasar Saliyo.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button