LabaraiNigeria

‘Yan ta’adda dubu 1 da 755 sun mika wuya a Najeriya – Sojoji

'Yan ta'adda dubu 1 da 755 sun mika wuya a Najeriya - Sojoji

Shalkwatar Tsaron Najeriya ta ce, akalla ‘yan ta’adda dubu 1 da 755 ne suka mika wuya cikin makwanni biyu, yayin da sojoji suka kashe 29 daga cikinsu tare da cafke wasu 55, baya ga fararen hula 52 da aka kubutar daga hannun mayakan a yankin arewa maso gabashin kasar.

Darektan Yada Labaran Shalkwatar Tsaron, Manjo Janar Benard Onyeuko ya sanar da haka a yayin gabatar da jawabin da suka saka yi makwanni biyu-biyu kan ayyukansu, inda ya ce, dakarunsu sun kuma kwato makamai daga hannun ‘yan bindigar da suka hada da bindigogi samfurin AK-49 da  AK-47 da alburusai da babura da kuma wayoyin salula.

A cewarsa, Rundunarsu ta yi wa mayakan Boko Haram  da na ISWAP kwanton-bauna akan hanyar Uzoro-Gadamayo da ke jihar Adamawa.

Kazalika sojojin tare da hadin-guiwar ‘yan sa-kai na Civilian Joint Task Force sun kama wasu mutane da ke yi wa ‘yan ta’addar safarar kayayyakin amfani, inda aka bayyana sunayensu da Hussain Dungus da Ali  Bulama Jidda da Malam Ali Abuna.

Daga cikin kayayyakin da aka gano a hannun wadannan ‘yan safarar har da kudin da yawansa ya kai Naira miliyan 1 da dubu 797 da kuma 700, sai kuma nau’ukan abinci da wayoyin salula da babura da dai sauransu.

Har ila yau, sojojin na Najeriya sun yi luguden wuta kan ‘yan ta’addar a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda suka ce, sun kashe wani kwamandan ISWAP mai suna, Alhaji Modu da aka fi sani da Bem Bem da kuma wasu mayakansa 20.

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan wannan lamari don jin tabakinku zamuso  kubiyomu kaitsaye ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.

Kada kuma ta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

 

 

 

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button