Nigeria
Trending

’Yan Sanda Sun Ceto Dan Shekara 50 Da Aka Sace A Jigawa

’Yan Sanda Sun Ceto Dan Shekara 50 Da Aka Sace A Jigawa

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya fitar ranar Talata.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 2:30 na rana, inda wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan Musa Barma suka yi awon gaba da shi.

Ya ce bayan samun labarin, ’yan sandan sun gano su, suka yi musu kwanton bauna a kan hanyar da ’yan bindigar suka bi a kusa da kauyen Arbus a Karamar Hukumar Kaugama.

Ya bayyana cewa, sakamakon musayar wuta da ’yan bindigar, ‘yan sanda, sun yi nasarar ceto wanda aka yi garkuwa da shi ba tare da ya ji rauni ba, yayin da maharan suka tsere zuwa cikin daji.

Shiisu, ya ce an kama mutum daya mai suna Nura Ahmad a unguwar Abuja a Karamar Hukumar Malam Madori wanda ake gudanar da bincike a kansa.

Ya ce an mayar da binciken lamarin zuwa hedikwatar SCIID domin gudanar da bincike mai zurfi.

Read also

Sojin Kamaru sun kashe fararen hula 10 a yankin ‘yan aware- Rahoto APS News Hausa.

 

Sojoji Sun Kona Kasuwar Boko Haram A Borno

Sojin Kamaru sun kashe fararen hula 10 a yankin ‘yan aware- Rahoto APS News Hausa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button