Labarai
Trending

Sojoji Sun Kona Kasuwar Boko Haram A Borno

Sojoji Sun Kona Kasuwar Boko Haram A Borno

Dakarun runduna ta 21 da ke garin Bama sun kai samame a kasuwar da ke bayan garin ne a ranar Litinin, suka kashe ’yan ta’adda hudu, suka jikkata wasu, ciki har da mata, sannan suka banka wa kasuwar wuta.Hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta ce, “An jikkata wasu mata hudu da ake zargin matan ’yan ta’addan Boko Haram kuma suna samun kulawa a Babban Asibitin Bama.”

Daraktan Yada Labaranta, Manjo-Janar Benard Onyeuko, ya ce ’yan ta’addan na hango su suka bude musu wuta, amma sojojin sun murkushe su, wanda hakan ya sa wasunsu tsere daga kasuwar.

“Nan take aka kashe ’yan ta’addar ISWAP/Boko Haram hudu wasu kuma suka mika wuya saboda tsanannin karfin wutar sojojin da ta sa yawancinsu guduwa zuwa daji.”

Sanarwar ta Manjo-Janar Benard Onyeuko ta ce sojoji sun yi kasuwar dirar mikiya ne bayan sun samu bayanan sirri a game da ita.

Ya ce sojoji sun mamaye haramtacciyar Kasuwar Dambia da aka fi sani da Markas ne a yayin da suke gudanar da aikin sharar daji.

Sabbin labarai

Dadumi dumi: Sojoji sun Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Dadumi dumi: Sojoji sun Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Dadumi dumi: Sojoji sun Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button