NigeriaWorld News

Sojin Kamaru sun kashe fararen hula 10 a yankin ‘yan aware- Rahoto APS News Hausa.

Sojin Kamaru sun kashe fararen hula 10 a yankin 'yan aware- Rahoto APS News Hausa.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta yi ikirarin cewa Sojin Kamaru sun kashe sun kashe mutane akalla 10 yayin sumamen da suka kai yankunan ‘yan awaren kasar da ke amfani da turancin Ingilishi.

Cikin wani rahoto da kungiyar ta fitar a yau kan take hakkin da ke faruwa a yakin da ake gwabzawa tsakanin Sojin na Kamaru da ‘yan tawayen na Ambazonia ta ce a baya-bayan nan Sojin sun kaddamar da wani sumame mai muni a yankin wanda ya kai ga cin zarafin tarin fararen hula.

Human Right Watch ta ce baya ga kisan mutanen 10 da Sojin Kamaru suka yi a yankin masu amfani da Turancin Ingilishi tsakanin 24 ga watan Aprilu zuwa 12 gaw watanYuni sun kuma aikata munanan laifukan kare hakkin dan adam.

Rahoton kungiyar ya ce a tsakanin ranakun Sojin kamaru sun kone gidaje 12 tare da lalata asibitocin yankin baya ga kame mutane 26 yayinda wasu fararen hula 17 suka bace.

Yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin Kamaru na matsayin matsuguni ga galibin masu amfani da turancin Ingilishi na Kamaru inda tun daga shekarar 2017 suka faro yakin neman ballewa daga Kamaru wanda ya haddasa asarar dimbin rayuka da kuma salwantar dukiyoyi.

Read Also:

Zan Karasa Aikin Da Buhari Ya Fara Na Cefanar Da NNPC — Atiku

JUST IN: Fuel Tanker Explodes In Lagos State.

Tirƙashi Ƴan bindiga sun sake afkawa iyalan Ango Abdullahi, sun sace sirikar sa da ƴaƴanta.

Dadumi dumi: Sojoji sun Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button