Labarai
Trending

Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci

Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci

Shahararriyar jarumar kasar Ghana Rosemond Alade Brown wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta karbi addinin Musulunci. Poloo ta Musulunta ne a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, bayan ta yi kalmar shahada tare da kadaita Allah.

Jarumar da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotunan dan kwarya-kwaryan taron da aka shirya na Musuluntarta tare da wasu malamai. Tuni mabiyanta suka shiga sashin sharhi domin tayata murna tare da yi mata barka da zuwa cikin addinin Musulunci.

Ga yadda ta rubuta a shafin nata: “Alhamdulillah na zama cikakkiyar Musulma yanzu godiya ga mataimakin limamin ASWAJ Ga West da babban limamin Nsakina Quran Reciter da ahlinsa kan taimakawa da suka yi wajen yiwuwar hakan ”

Kamar yanda ta rubuta a shafinta na istagram

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button