Labarai
Trending

Dadumi dumi: Sojoji sun Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Dadumi dumi: Sojoji sun Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Kaduna – Rundunar Sojojin saman Najeriya (NAF) ta halaka ƙasurgumin shugaban yan ta’adda, Alhaji Shanono, da wasu mayaƙansa guda 17 a jihar Kaduna, kamar yadda Leadership ta ruwaito. Alhaji Shanono da yan tawagarsa sun bakunci lahira ne a wurin wani taro a Ukambo, wani ƙauye mai nisan kilomita 131 daga Kaduna lokacin da jirgin rundunar Operation Whirl Punch ya musu luguden wuta ranar Talata.

Kakakin hukumar sojin saman, Edward Gabkwet, ya ce sama da bindigu 30, Babura 20 luguden wuta ya ragargaza yayin da wasu mutum 26 da ke tsare hannun yan ta’addan suka kubuta.

Yadda lamarin ya faru

Channels ta rahoto cewa Wannan na samame na ɗaya daga cikim nasarorin da hukumar doji ta samu a yankin, inda kakakin ya bayyana cewa:

Samamen da jirgin NAF ya kai ya yi sanadin sheƙe yan ta’adda da dama tare da rugurguza maɓoyarsu. Ɗaya daga cikin irin waɗan nan farmakin da Jirgi ya kai jiya 9 ga watan Agusta ya halaka sanannen shugaban yan ta’adda a Kaduna.” “Bayan samun bayanan sirri a jiya cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Alhaji Shanono, ya shirya taro da mayakansa a kauyen Ukambo kilomita 131 daga Kaduna, nan take Jirgin Operation Whirl Punch ya tashi zuwa wurin.”

“Da ya isa wurin ya hangi yan ta’addan, bayan sharar fage da gano babu fararen hula kusa, jirgin ya samu izini ya saki ruwan wuta. Bayanai daga yankin sun nuna cewa harin ya lalata bindigu sama da 30 da babura 20.”

Majiyar ta ƙara da cewa, “Yan ta’adda 18 cikin su har da Alhaji Shanono sun bakunci lahira, sauran kuma suka jikkata. Kaka kuma aƙalla fararen hula 26 da yan ta’adda ke tsare da su suka kubuta sanadin samamen.”

Asali: legit hausa.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button