LabaraiNigeria

Alhamdulilla: Najeriya ta mayar da ƴan gudun hijira sama da 100,000 gida daga Tafkin Chadi.

Alhamdulilla: Najeriya ta mayar da ƴan gudun hijira sama da 100,000 gida daga Tafkin Chadi.

Rundunar sojin Najeriya, ta ce sama da ‘yan gudun hijira 100,000 ne aka mayar da su gidajen su da ke gabar tafkin Chadi a wani bangare na nasarorin da aka samu kan ‘yan ta’adda a yankunan da ke kan iyakokin Najeriya, wato Nijar da Chadi da Kamaru.

Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), Manjo Janar Abdul Khalifah Ibrahim, shine ya bayyana hakan a barikin sojoji na Maimalari, da ke birnin Maiduguri yayin bikin mika lambar yabo ga jami’ai da sojoji da suka shiga aikin Operation Lake Sanity da aka kammala.

Ibrahim ya bayyana cewa an dawo da harkokin tattalin gudanarwa da zamantakewa a cikin al’umma da ke kauyukan da suka koma.

Ya ce, “Abubuwa suna sauki, muna samun raguwar hare-hare a wadannan yankuna, idan kuma aka samu raguwar hare-haren za a samu raguwar illolin da abin ke haifarwa. An samu raguwar hare-haren da ake kaiwa fararen hula sannan kuma an samu raguwar hare-haren hatta a wuraren da sojojinmu suke aiki kuma hakan na faruwa ne sakamakon karuwar hare-haren da sojoji ke kaiwa masu dauke da makamai.

“A cikin shekara guda da ta wuce a cikin yankunan tafkin Chadi, sama da mutane 100,000 ne suka koma gidajesu, mutanen da ko dai ‘yan gudun hijira ne a wasu kasashe ko kuma wadanda suka kasance na cikin giuda ne. Sun dawo wurare kamar su Banki, Cross Power, Baga, duk a cikin Najeriya suke. Idan ka je Nijar kamar Baroua, idan ka je Chadi kamar Bitiri da Kamaru kamar Amchibi da Gulafata mutanen sun koma kauyukansu,” inji shi.

“A hankali abubuwa suna ta sauki, harkokin tattalin arziki suna karuwa, makarantun da suke kusa da su an sake bude su, kasuwanni, asibitoci komai ya daidaita. Duk da yake ba za mu iya cewa komai akan ko yaki yak are ba, amma ba mu kasance kamar baya ba kuma muna samun ci gaba. Kuma wannan ba yaki ne da zamu gama a lokaci guda ba, ba abu ne mai sauki ba amma kuma muna aiki don ganin an fatattake su a duk inda suke.”

A halin da ake ciki, kwamandan rundunar ya kuma jagoranci yi wa hafsoshi da sojoji 850 ado da suka shiga ayyukan tsaftace yankin tafkin Chadi, inda ya kara da cewa, sashin na 1 na Operation Hadinkai ya tallafa wa ayyukan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa da wani bataliyar da ya yi aikin share fage da dama.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Kucigaba da bibiyarmu a shafinmu na APS News Hausa domin samun sabbin rahotanni mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button