Labarai

Tirƙashi Ni ne a bidiyon da aka kama ‘yan luwadi, amma zan yi karin bayani, Yahaya Shareef.

Tirƙashi Ni ne a bidiyon da aka kama ‘yan luwadi, amma zan yi karin bayani, Yahaya Shareef.

 

Wani fitaccen dan TikTok da Instagram, Yahaya Shareef ya bayyana cewa shi ne a cikin wani bidiyo wanda ake ta yadawa wanda ‘yan sanda su ka titsiye ‘yan luwadi a Jihar Kano, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Matashin wanda ya samu shahara a kafafen sada zumuntar zamani ya dade yana daukar hankalin jama’a tun daga kyawun siffarsa da kuma iya sanya suttura.

yahaya

Har ila yau, ana ganin hotuna da bidiyonsa a Dubai, Saudi Arabia da sauran kasashe, wani lokacin ma har tare da ‘yan uwansa da mahaifiyarsa.

Ana ganinsa yana rike da tsadaddun wayoyi a cikin falo da dakuna na alfarma inda yake hawa kan wakoki tare da kwasar rawa.

Sai dai kwatsam sai ga wani bidiyo ya bayyana wanda ‘yan sanda su ka titsiye shi a matsayin daya daga cikin wadanda ake zarginsu da aikata luwadi da damfara.

Ganin bidiyon ya fara bazuwa ne yayin da wasu ke cewa shi ne wasu kuma su na musantawa yasa ya fito fili ya bayyana gaskyar abinda ya sani.

A cewarsa, tabbas shi ne a cikin bidiyon amma idan jama’a sun kula dakyau bai amsa laifin yin luwadi ko kuma damfarar kowa ba.

Ya ce ko a lokacin ‘yan sanda ne su ka tasa shi gaba inda su ka tilasta masa amsa laifin da bai aikata ba. Amma kuma lokaci ya yi da zai yi bayani dalla-dalla.

A cewarsa, shekaru 4 kenan da faruwar lamarin kuma wasu ne su ka shirya hakan musamman don tozarta shi, amma a lokacin da yayi bidiyon yana wani aiki ne, daga baya zai natsu ya fallasa sunaye.

Ya ce Allah ya rufa masa asiri don kasuwancinsa yake yi. Idan akwai wanda ya san ya neme shi, ya fito ya bayyana wa duniya.

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button