Nigeria

Justice Ibrahim Muhammad Tanko ya ajiye aiki ne saboda lalura na rashin lafiya, wanda sanin kowa ne mutumin nan yana da ingantaccen lafiya Gaskiyar Magana.

Justice Ibrahim Muhammad Tanko ya ajiye aiki ne saboda lalura na rashin lafiya, wanda sanin kowa ne mutumin nan yana da ingantaccen lafiya Gaskiyar Magana.

 

NIGERIA KENAN

Kwanaki biyu da suka wuce an wayi gari da wani labari mai ban mamaki cewa Alkalin Alkalan Nigeria Chief Justice of Nigeria (CJN) Justice Ibrahim Muhammad Tanko GCON ya ajiye aiki sakamakon wai rashin lafiya

Daga cikin manyan aikin Alkalin Alkalan Nigeria (CJN) shine idan an samu rashin aminci a tsakanin ‘yan takaran Shugaban Kasa lokacin zabe, to shine zai zartar da hukunci na karshe akan wanda yake ganin ya cancanta

Amma abinda ya bawa ‘yan Nigeria mamaki shine cewa da akayi wai Justice Ibrahim Muhammad Tanko ya ajiye aiki ne saboda lalura na rashin lafiya, wanda sanin kowa ne mutumin nan yana da ingantaccen lafiya, kuma ba laifi ya aikata ba, domin da laifi yayi ko cin amana Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ba zai bashi lambar yabo na GCON ba

Justice Ibrahim Tanko Muhammad asalinsa dan jihar Bauchi ne, kuma ba wai kawai dan boko bane zallah, Malamin addinin Musulunci ne, har Tafisirin Qur’ani yana gabatarwa duk shekara a watan Ramadan idan yazo Bauchi

Gashi yanzu sun tilasta koransa daga aiki Billahi ba don yana so ba, sun kawo wani dan uwan wanda suke son ya zama shugaban Kasa, ku ziyarci Wikipedia page na wanda suka kawo wanda aka kirkiri Wikipedia page dinsa a 2015, zaku ga rashin gaskiya kamar haka:
-A shekarar 2016 anyi editing wikipedia page dinsa sau 2.
-A shekarar 2017 anyi editing sau 1
-A shekarar 2018 anyi editing sau 4
-A shekarar 2019 anyi editing sau 2
Daga shekaran jiya zuwa yau sunyi editing Wikipedia page dinsa sau 22

Sannan zaku ga rashin gaskiya a takardun mutumin da suka wanda shekarun haihuwarsa ya nuna cewa an haifeshi a shekarar 1958, amma wai ya fara karatu a 1959, tsakanin haihuwarsa da fara karatunsa shekara 1 kenan saboda sun raina mana wayo

Na samu bayanan sirri ingantattu game da ajiye aiki da wannan Ibrahim Tanko yayi, amma wanda suka tsara wannan abin sunyi babbar mantuwar abinda ya faru a zaben 2015 akan yadda Allah Ya nuna ikonSa, kuma sun manta cewa Allah ne yake bada mulki, mummunan shirin murdiya da suke a zaben 2023 ba zaiyi tasiri ba da karfin ikon Ubangiji SWT

Yadda Allah Ya wargaza musu Plan A dinsu, yanzu suka dawo kan Plan B, Insha Allahu shima Allah Zai wargazashi, babu nasara ga wadanda sukaci amanar ‘yan Nigeria

Yaa Allah Ka kare talakawan Nigeria daga sharrin maciya amana, Allah Ka haramtawa masu shirin murdiyan zabe nasara har abada.

Read Also:

Innalillahi wainnailai raji’un Rayuwa Babu Tabbata; Mutuwar Jarumin kannywood Rabi’u Rikidawa Gaskiyar lamari.

Innalillahi wainnailai raji’un Rayuwa Babu Tabbata; Mutuwar Jarumin kannywood Rabi’u Rikidawa Gaskiyar lamari.

Innalillahi wainnailai raji’un Rayuwa Babu Tabbata; Mutuwar Jarumin kannywood Rabi’u Rikidawa Gaskiyar lamari.

Innalillahi wainnailai raji’un Rayuwa Babu Tabbata; Mutuwar Jarumin kannywood Rabi’u Rikidawa Gaskiyar lamari.

To jama’a kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button