Advertisement
Kannywood News

Tofa! Harkar Fim A Yanzu Mun Yi Girman yazama Dole Mu Bar Wa Yara – cewar shu’aibu Lilisco.

Tofa! Harkar Fim A Yanzu Mun Yi Girman yazama Dole Mu Bar Wa Yara – cewar shu'aibu Lilisco.

FITACCEN jarumin Kannywood Shu’aibu Idris (Lilisco) ya bayyana cewa shi a yanzu harkar fim ya bar wa na baya, sai dai ya riƙa fitowa a matsayin manya kuma ya zamo mai bada shawara ga matasa masu tasowa.

Lilisco, wanda ya ƙware a wajen koyar da rawa kafin ya ƙara haske a fagen fitowa a matsayin jarumi, ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da mujallar Fim ta yi da shi a matsayin sa na tsohon ɗan wasa da ya jima ana damawa da shi a cikin harkar.

Ya ce, “To mu a yanzu sai dai mu yi godiya ga Allah da ya sa mu ka samu kan mu a wannan lokacin da wasu abubuwa sai dai mu ga ana yi. Domin kuwa a baya mu ake kallo, kuma wasu abubuwan ma idan ba mu ne mu ka yi ba, to ba zai yiwu ba.

Ya ƙara da cewa: “A a wancan lokacin ka ga idan ana maganar rawa ta zamani da ta gargajiya, ai mu ne masu yi kuma mu ne masu koyar da ita. Shi ya sa a lokacin mu ake kallo, mu ne jaruman.

“Amma a yanzu fa? Wasu ake yayi, su ne su ke cin lokacin su. To, ka ga kowa da lokacin sa. Don haka a yanzu ko da za mu fito a fim sai dai a matsayin iyaye ko wani rol ɗin da ya dace da babban mutum, shi ya sa za ka ga a finafinan da na ke fitowa a yanzu na fi fitowa a jami’in tsaro ko wani ma’aikacin ofis.”

Dangane da yadda harkar fim ta ke a yanzu kuwa wajen rashin tsari, jaruɓin ya ce, “Ai duk wannan abin yawa ne ya jawo hakan, domin a wancan lokacin ba mu da yawa, sai ka ga idan darakta biyu su na aiki to sun ɗebe jaruman masana’antar da sauran masu aiki, sai ka ga babu kowa. Amma a yanzu idan darakta ashirin su na aiki lokaci guda idan ka zo sai ka ga kamar ma wasu ba su tafi aiki ba.

“To, don haka an yi yawa, dole a samu rashin tsari. Wannan kuma ya sa aka samu raunin shugabanci.”

Advertisement

A kan batun makomar harkar fim kuwa, Lilisco ya ce, “Makomar ta mai kyau ce ga wanda ya yi abu mai kyau, domin saboda mun yi abu mai kyau shi ya sa mu ka kawo har yanzu ana damawa da mu.

“A yanzu ga shi mun yi aure mun yi ‘ya’ya duk a cikin harkar fim ɗin. Don haka fatan mu sai dai Allah ya ba mu cikawa da imani, Allah ya raya zuriyar mu, ya kyautata bayan mu.

Read Also:

I’ll seek Benue people’s consent to arm guards if FG withholds licence – Ortom.

Tofa! Fargabar ta’addanci ta tilasta tsaurara tsaro a gidajen yarin Zamfara Kebbi da Katsina Baki Ɗaya.

Shugaban kungiyar mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad ya sha alwashin kai hari a birnin Tel Aviv bayan wani harin da Isra’ila ta kai ta tare da kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar a zirin Gaza, yayin da mutane 44 suka jikkata.

Tofa! Ƙasar Morocco Ta ƙara aikewa da wasu karin bakin haure gidan yari Tirƙashi.

To jama’a kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Advertisement

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button