Advertisement
World News

Tofa! Ƙasar Morocco Ta ƙara aikewa da wasu karin bakin haure gidan yari Tirƙashi.

Tofa! Ƙasar Morocco Ta ƙara aikewa da wasu karin bakin haure gidan yari Tirƙashi.

Kasar Maroko ta yankewa wasu bakin haure 14 hukuncin daurin watanni takwas bayan kamasu kwana guda gabanin yunkurin tsallakawa zuwa yankin Melilla na kasar Spain a watan Yuni.

Hukunci ne mai tsananin gaske,  a cewar Lauyansu Mbarek Bouirig, inda ya ce suna shirin daukaka kara.

An kama wadanda ake zargin galibi ‘yan kasar Sudan mai fama da talauci ne a ranar 23 ga watan Yuni a yayin wani farmakin da jami’an kasar Morocco suka kai a kusa da garin Melilla, tare da wasu yankunan kasar Spain na Ceuta, wato iyakar kasa daya tilo da Tarayyar Turai ta yi da Afirka.

Akalla bakin haure 23 ne suka mutu washegari yayin da kusan mutane 2,000, da yawa kuma ‘yan Sudan suka kutsa cikin shingen kan iyaka. Wannan dai shi ne adadin wadanda suka mutu mafi muni a cikin shekaru da dama da aka samu na masu yunkurin tsallakawa cikin yankunan.

Bouirig ya ce an tuhumi mutanen 14 da laifukan da suka hada da na wata kungiyar shige da fice da kuma cin mutuncin jami’an tsaro.

Omar Naji jami’in kungiyar kare hakkin bil’adama ta AMDH da ke sa ido a kan shari’ar ya ce bakin hauren ba su yi kokarin tsallakawa kan iyaka ba.

Advertisement

Ko a watan da ya gabata, wata kotu a Morocco ta yanke wa wasu bakin haure 33 hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 11 bisa samun su da shiga kasar ba bisa ka’ida ba, yayin da ake ci gaba da wata shari’ar ta daban kan wasu ‘yan ci-rani 29 ciki har da kananan yara.

Wata Kungiyar kare hakkin  bil’adama ta kasar Spain da ake kira Caminando Fronteras ta ce mutane kusan 37 ne suka rasa rayukansu a yunkurin tsallakawa Turai, fiye da adadin mutane 23 a da aka sani hukumance.

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi Allah wadai da amfani da karfin da ya wuce kima da jami’an tsaron Morocco da na Spain suke a kan bakin haure.

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye. 

Kucigaba da bibiyarmu a shafinmu na APS News Hausa Appsoft.com.ng Domin samun sabbin shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa.

Read Also:

Eligibility criteria for the Vanier Canadian International Scholarships//2022.

TirKashi: Kungiyar IPOB sun Kashe Yan Nijar 8 

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu Nasarar kama wani Matashi da yayi Garkuwa Da ɗan makwaftansu.

Wata Budurwa Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Rataye Kanta data’yi Bisa Zargin Iyayen ta Na Shirin Yi Mata’ Auren Dole’ a jihar Kano.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button