Shugaban kungiyar mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad ya sha alwashin kai hari a birnin Tel Aviv bayan wani harin da Isra’ila ta kai ta tare da kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar a zirin Gaza, yayin da mutane 44 suka jikkata.
Shugaban kungiyar mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad ya sha alwashin kai hari a birnin Tel Aviv bayan wani harin da Isra'ila ta kai ta tare da kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar a zirin Gaza, yayin da mutane 44 suka jikkata.

Shugaban kungiyar mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad ya sha alwashin kai hari a birnin Tel Aviv bayan wani harin da Isra’ila ta kai ta tare da kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar a zirin Gaza, yayin da mutane 44 suka jikkata.
Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda suka mutu a sakamakon harin bayan babban jagoran na mayakan Falasdinawan, akwai mutane 15, yayin da gidajen mutane da dama suka ruguje.
An hango yadda bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya bayan harin, abin da ya tunzura hukumomin Gazan da ke ganin hakan tamkar wata takalar fada.
A cewar kungiyar tuni aka yi jana’izar babban kwanadan, Tayseer Al-Jabari Abu-Mahmud, wanda ya mutu da safiyar ranar Juma’a ta cikin sanarwar da kungiyar ta fitar.
Dakarun Gaza da wasu kananan yara hudu na cikin wadanda suka rasa rayukansu tare da jagoran a harin da Isra’ilan ta kai.
Tuni dai kakakin rundunar sojin Isra’ila ya ce, yanzu Gaza ta fara ganin irin wadannan hare-hare, don kuwa ba za ta gaza ba har sai ta kakkabe mayakan baki daya daga yankin.
Read Also:
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu Nasarar kama wani Matashi da yayi Garkuwa Da ɗan makwaftansu.
Achievement International Scholarships at Columbia College //2022
Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.