Labarai
Trending

Wata sabuwa: gwamnan kogi ya hana karuwanci a jihar

Wata sabuwa: gwamnan kogi ya hana karuwanci a jihar

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bada umurnin a rufe dukkan gidajen da karuwai ke zama a jihar. Ya kuma haramta saka takunkumin fuska a wuraren da al’umma ke taruwa saboda a rika gane kowa a jihar.

Hakan ya biyo bayan wasu matsalolin tsaro ne da aka samu a jihar a baya-bayan nan, The Punch ta rahoto.

Ya bada umurnin ne a ranar Talata a Lokoja yayin wani taro da aka yi da sarakuna masu sanda mai daraja ta ɗaya da biyu da ma shugabannin ƙananan hukumomi. Bello ya kuma bada umarnin rushe wasu kanguna a Lokoja, Osara, Zango, Itobe, Obajana da dukkan sassan jihar.

Ya umurci kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, shugabannin ƙananan hukumomi, shugabannin kungiyoyi da jami’an tsaro su gana da masu adaidaita sahu don tantance su da daukan bayanan su.

Gwamnan ya kuma bukaci masu sarautun gargajiya su tsare garuruwansu su kuma tabbatar an tsefe dukkan lunguna da saƙuna.

Tabbatar da zama lafiya a yankunan ku aikin ku ne. Nauyi ya rataya a kanku ku kawar da dukkan laifuka a yankunan da ke karkashin ku,” in ji gwamnan. Ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan jami’an tsaro da aka kashe a karamar hukumar Ajaojuta a ranar Asabar da ta gabata.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button