World News
Trending

Ana fargaba a duniya kan yiwuwar fadowar kumbon da China ta harba sararin samaniya

Ana fargaba a duniya kan yiwuwar fadowar kumbon da China ta harba sararin samaniya

Ana sa ran tarkacen kumbon da China ta harba sararin samaniya zai faɗo duniyarmu ta Earth a ƙarshen makon nan.

Sai dai barazanar yiwuwar faɗawarsa yanki mai cike da jama’a ba ta da yawa.

Amma hakan ya sanya tambayoyi a kan yadda kowace ƙasa za ta kwashi rabonta na tarkacen kumbon.

A baya Nasa ta sha kiraye-kiraye kan hukumar sararin samaniyar China, cewa ta tsara kumbunanta ta hanyar ɓangarorinsa su kasance ƙanana a yayin kutsawa samaniyar, saboda haka tsarin ƙasa da ƙasa yake.

Kumbunan China da a baya-bayan nan ake harba su tasharta da ke sararin samaniya wacce ba a kammala ta ba mai suna Tiangong, ba sa iya kutsawa saman yadda ya kamata.

A ranar Lahadi ne ta sake harba kumbon na bayan nan, mai suna Long March 5, ɗauke da ɗakin gwaje-gwaje zuwa tashar Tiangong.

A ranar Laraba gwamnatin China ta ce harba kumbon ba zai zama barazana ga mutanen da ke doron duniya ba saboda ga dukkan alamu a teku zai faɗa.

Kazalika, akwai yiwuwar tarkacen kumbon za su iya faɗowa ƙasa a yankin da ke cike da jama’a, kamar yadda ya faru a watan Mayun 2020 lokacin da tarkacen ya faɗa kan wasu ƙadarori a ƙasar Ivory Coast har suka lalace.

A yanzu haka dai kumbon wanda babu komai a cikinsa yana ta zagaye a saman duniya inda ake jawo shi don ya faɗo doron duniyar.

Wata hukumar kula da sararin samaniya mai zaman kanta ta Aerospace Corporation, da ke da cibiya a California, ta ce zai faɗo duniyar ne da misalin ƙarfe 12.24 na dare agogon GMT ranar Lahadi,

Ya yi wuri a san inda tarkacen mai yawan ton 25 zai faɗa.

Akwai yiwuwar tarkacen ka iya faɗa wa wasu yankuna a Amurka ko Afirka ko Australiya ko Brazil ko Indiya ko Kudu maso gabashin Asiya, a cewar hasashen hukumar.K

Karinsabbin labari

RE: Parents Withdraw Students From Bingham University Over Fear Of Boko Haram Attack In Nigeria.

Za Mu Binciki Malamin Da Ya Daki Dalibarsa Da Gora —Gwamnatin Kaduna

RE: Parents Withdraw Students From Bingham University Over Fear Of Boko Haram Attack In Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button