Labarai

Christian – Christian: Ɗan takarar LP Peter Obi ya zaɓi Christa Doyin Okupe a matsayin abokin takararsa

Christian - Christian: Ɗan takarar LP Peter Obi ya zaɓi Christa Doyin Okupe a matsayin abokin takararsa

Ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya zaɓi Doyin Okupe a matsayin mataimakinsa na riƙo kafin ya yanke shawarar wanda zai zaɓa.

LP ta miƙa sunan Mista Okupe ga hukumar zaɓe INEC yayin da wa’adin da hukumar ta bai wa jam’iyyu ke ƙarewa a daren yau Juma’a.

Doyin Okupe, shi ne tsohon mai tamaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan kan kafofin yaɗa labarai.

“Yanzu haka da nake magana da ku, ni nake riƙe da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party,” a cewar Okupe yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yau Juma’a.

Okupe ya tabbatar da cewa Mista Obi na ci gaba da shawarwari game da wanda zai zaɓa a matsayin abokin takarar tasa.

Hukumar ta saka yau Juma’a 17 a matsayin rana ta ƙarshe da jam’iyyu za su miƙa mata sunayen ‘yan takarar da suka zaɓa da za su wakilce su a zaɓen 2023, amma suna iya sauya sunayen mataimakan ‘yan takarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button